Saturday, 22 October 2016

Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutum 70 a Kamaru

Shugaban Kamaru Paul Biya ya tabbatar da
mutuwar mutum 70 a mummunan hadari jirgin
kasar da y

a faru a kasar ranar Juma'a.
Paul Biya ya bayyana haka ne a wata sanarwa da
ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shugaban kasar ya kara da cewa mutum 600 sun
samu raunuka a hadarin wanda ya faru lokacin
da jirgin ya kaucedaga kan layinsa a yankin
Eseka wanda ke tsakanin manyan biranen kasar
biyu - Douala da Yaounde.
Mr Biya ya ce, ''Na bai wa jami'an gwamnati
umarnin bayar da taimako ga mutanen da suka
tsira daga hadarin jirgin, yayin da ake ci gaba da
bincike domin gano musabbabin hadarin jirgin.''
Jirgin dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin
Douala daga babban birnin kasar wato Yaounde.
Wakilinmu a kasar ta Kamaru ya ce an kiyasta
cewa kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da
jirgin ya kauce daga kan layinsa.

No comments:

Post a Comment