Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya umarci
a gudanar da binciki kan zargin yin lalata da 'yan
gudun hijirar Boko Haram da kungiyar Human
Rights Watch (HRW) ta yi.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce
shugaban ya kadu da jin wannan labari.
Sannan ya ce "kyautata jin dadin rayuwar
wadannan mutane da ke fuskantar barazana
abu ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa".
Sanarwar wacce mai magana da yawun
shugaban, Garba Shehu ya sanya wa hannu,
ta ce 'yan Najeriya dama kasashen duniya su
san cewa gwamnati ba za ta dau zargin na
kungiyar ta HRW da wasa ba.
Shugaba Buhari ya bai wa babban Sipeton
'yan sandan kasar da gwannonin jihohin da
lamarin ya shafa umarnin su gaggauta
gudanar da bincike game da batun.
Binciken na su shi zai nuna mataki na gaba
da gwamnatin za ta dauka, a cewar
sanarwar.
A ranar Litinin ne kungiyar HRW ta zargi
wasu jami'an gwamnatin Nigeria da yin lalata
da 'yan matan da rikicin Boko Haram ya raba
da muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da
yaudararsu don yin lalata da su.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da rashin
yin abin da ya kamata wajen kare irin
wadannan matan.
Ta kara da cewa ta samu bayanin yin lalata
da kuma fyade kan mata da 'yan mata 43 da
ke zaune a sansanonin gudun hijira bakwai
da ke Maiduguri, a jihar Borno.
Sama da mutane miliyan biyu ne suka bar
gidajensu sakamakon rikicin na kungiyar
Boko Haram.
Ahmad salihu ahmad
Tuesday, 1 November 2016
Nigeria: Za a yi bincike kan lalata da 'yan gudun hijira
Saturday, 22 October 2016
Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutum 70 a Kamaru
Shugaban Kamaru Paul Biya ya tabbatar da
mutuwar mutum 70 a mummunan hadari jirgin
kasar da y

a faru a kasar ranar Juma'a.
Paul Biya ya bayyana haka ne a wata sanarwa da
ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shugaban kasar ya kara da cewa mutum 600 sun
samu raunuka a hadarin wanda ya faru lokacin
da jirgin ya kaucedaga kan layinsa a yankin
Eseka wanda ke tsakanin manyan biranen kasar
biyu - Douala da Yaounde.
Mr Biya ya ce, ''Na bai wa jami'an gwamnati
umarnin bayar da taimako ga mutanen da suka
tsira daga hadarin jirgin, yayin da ake ci gaba da
bincike domin gano musabbabin hadarin jirgin.''
Jirgin dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin
Douala daga babban birnin kasar wato Yaounde.
Wakilinmu a kasar ta Kamaru ya ce an kiyasta
cewa kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da
jirgin ya kauce daga kan layinsa.

Subscribe to:
Posts (Atom)